Isa ga babban shafi
Najeriya

Kasa ta binne mahaka ma’adinai 9 a Zamfara

Rahotanni Daga Jahar Zamfara a Shiyar arewa maso yammacin Najeriya, sun ce akalla mutane Tara kasa ta rufe a kauyen Ruwan Dorawa, karamar hukumar Mulki taMaru, yayin da suke kokarin hako zinare ba tare da izini ba.

Masu hako ma'adinai a Jahar Zamfara Najeriya
Masu hako ma'adinai a Jahar Zamfara Najeriya RFI
Talla

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wasu mutane biyu sun yi nasarar hako zinar da kudin sa ya kai Naira Miliyan Biyu da Dubu Dari Uku.

Bayanai sun ce, da Asubahi aka yi kururuwar kai dauki ga mahakan goma da kasa ta binne, amma ba’a iya ciro su ba sai da azahar, kuma kafin nan mutane 9 sun mutu, Mutum daya ne ya tsira da ransa, kuma yana waknce a gadon asibiti.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.