Isa ga babban shafi
Algeria

An yiwa kudin tsarin mulki kwaskwarima a Algeria

Majalisar dokokin Algeria ta amince da kudirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima da hukumomi ke ganin zai karfafa demokradiyya a kasar yayin da ‘yan adawa suka nuna rashin gamsuwarsu da shirin.

Abdel Aziz Bouteflika ,Shugaban kasar Algeria
Abdel Aziz Bouteflika ,Shugaban kasar Algeria AFP PHOTO / Fayez NURELDINE
Talla

Kudirin dai ya bukaci takaita wa’adin shugabancin kasar zuwa biyu.
Sannan ya haramta wa ‘Yan asalin kasar da ke da shaidar zama ‘yan wasu kasashen neman babban mukamin siyasa.

Shugaban kasar Abdel Aziz Bouteflika da aka zaba a karo na farko a shekara ta 1999 da shekara 2004 ne ya shigar da wannan bukata zuwa yan Majalisun kasar.
Yan siyasa daga cikin gida dama wajen kasar na ci gaba da nuna adawa a kai,Sai dai Gwamnatin kasar ba ta ce upon ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.