Isa ga babban shafi
Algeria-Alkaida

Kungiya Aqmi mai alaka da Alkaida a nahiyar Afrika ta kashe dakarun Algeria 9

Rundunar sojan kasar Algeriya ta yi hasarar kimanin dakarunta 9 a wanin kwanton Bauna da mayakan jihadin kungiyar Al-ka’ida a kasashen larabawan yankin Magrib Islamik (Aqmi) ta dau alhakin kai wa.

dakarun sojan Aljeriya a yankin kudancin kasar.
dakarun sojan Aljeriya a yankin kudancin kasar. AFP PHOTO/ENNAHAR TV
Talla

kungiyar ta Aqmi wace ta bayyana kashe dakaru 14 a harin dake cikin jerin hare haren da take kai wa kan dakarun sojan gwamnatin kasar ta Algeria yau da kimanin shekara guda da ta gabata

Ofishin ministan tsaron kasar ta Aljeriya ya bayyana matukar bakin cikinsa, dangane da harin da ya yi awan gaba da rayukan dakarun 9 da ya danganta da cewa sun mutu ne a matsayin shahidan kasar a cikin harin da mayakan jihadin suka kai masu a marecen ranar juma’ar data gabata a lardin Ain-Defla, mai tazarar kilo mita 150 Kudu maso yammacin Alger babban birnin kasar ta Algeriya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.