Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus zata kafa sansani ajiye ‘Yan kasar Algeria da Morocco

Kasar Jamus na shirin kafa wani sansani da zata dinga ajiye ‘yan kasar Algeria da Moroko wadanda aka ki amincewa da bukatar su na samun mafaka, kafin tusa keyar su zuwa kasashen su.

Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel 路透社
Talla

Jaridar kasar Welt am Sonntag ta ruwaito cewar shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da shugaban Jihar Bavaria Horst Seehofer sun amince cewar kar a sake baiwa ‘yan kasashen biyu matsuguni a fadin kasar.

Kasar Jamus ta ce bukatar ta itace taimakawa wadanda yaki ya tilastawa barin kasar su, ba wadanda ke barin kasashen su ba domin shiga turai ba tare da wasu kwararran Hujojji ba.

Kasashen Turai a koda yaushe na sake bijiro da sabbin matakan dakile matsalar Bakin haure dake cigaba da Kwarara Nahiyar su, yayin da Angela Merkel Waziriyar Jamus ke fuskantar kalubali daga al'umma Kasar masu adawa da matakan karban Bakin hauren.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.