Isa ga babban shafi
Turai-Jamus

Bakin haure na ci gaba da tsallakawa zuwa Jamus

Akalla Bakin haure 1,000 suka isa Bavaria dake kudancin kasar Jamus daga Austria duk da dokar rufe kan iyakokin kasar da ta sanar a karshen makoA dai dai lokacin da ministocin harkokin cikin gida na kungiyar kasashen Turai ke shirin gudanar da wani taro a Brussels kan batun rarraba bakin haure a tsakanin su, hukumomin Jamus sun sanar da tsaurara matakai akan iyakokin kasar domin rage kwararar bakin zuwa cikin kasar.

Wasu bakin haure dake kan hanyar zuwa Jamus
Wasu bakin haure dake kan hanyar zuwa Jamus 路透社
Talla

Mai Magana da yawun Yan Sandan Jamus, Rainer Scharf yace har yanzu daruruwan baki na tsallakawa daga Austria suna shiga Jamus, kuma ya zuwa daren jiya sun lissafa kusan 1,000.

Akalla baki 63,000 suka isa Munnich ta tashar jiragen kasa.

Kasashe irinsu Slovakia da Jamhuriyar Czech na cikin kasashen dake  adawa da shirin rarraba bakin hauren tsakaninsu.
Kwamishinan kula da hijira da ayyukan cikin gida na Tarayyar Turai Dimitris Avramopoulos ya ce ya zama wajibi ga kasashen sun hada kai idan suna son magance matsalar bakin-haure da ke ci gaba da kwarara a Turai.
Hukumar za ta gabatar da adadin ‘Yan gudun hijirar da kowace kasa za ta karba tsakanin mambobin kungiyar.
Jamus ta amince za ta karbi kashi 20 na ‘Yan gudun hijirar Syria kimanin 31,400.
Faransa ma ta amince za ta karbi 24,000, Birtaniya 20,000, yayin da Spain ta amince ta karbi 14,900
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.