Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Faransa da Jamus sun amince da matakan rage karban Bakin haure

A wata wasikar hadin-gwiwa da suka aika wa hukumar tarayyar Turai, kasashen Faransa da Jamus sun amince da bukatar matakan rage karban bakin haure da ke Kwarar Turai.

Shugaban gwanatin Jamus Angela Merkel da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban gwanatin Jamus Angela Merkel da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande 路透社
Talla

Wasikar da aka rubuta a ranar 3 ga watan wanann Disamba, Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Cazeneuve da takwaransa na Jamus Thomas de Maiziere sun bukaci hukumar da ke kula da kan iyakokin kasashen turai wato FRONTEX ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasashen.

Ministocin sun ce, ya kamata hukumar FRONTEX ta yi aiki da jami’an tsaro na musammam a lokacin bukatar gaggawa tare da samun bayanan tsaro na sirri na kasashen tarayya Turai.

A cewar ministoicin ba su amince da alakanta ‘yan gudun hijira da ‘yan ta’adda ba da wasu ke yi, kuma sun caccaki Jan kafan da ake samu wajen gina sansanin ‘yan gudun hijira.

Batun karbar ‘yan gudun huijira dai na ci gaba da raraba kawunan masu ruwa da tsaki tun lokacin da aka bayyana cewa mutanen da suka kai hari a birnin Paris na Faransa a watan jiya, sun shiga Turai ne ta hanyar da bakin haure ke shiga.

A wannan makon ne kasar Jamus ta sanar cewa ta karbi ‘yan gudun hijira kimanin 960,000 a wannan shekara ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.