Isa ga babban shafi
EU-Amurka-Iran

Macron na son jagorantar tawagar EU don sasanta Amurka da Iran

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi jagorantar yunkurin Tarayyar Turai don shiga tsakani, da nufin warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Iran da Amurka, dai dai lokacin da EU ke neman hanyoyin tunkarar rikicin don warware shi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Koji Sasahara/Pool via REUTERS
Talla

Shugaba Emmanuel Macron ya fito karara ya nuna bukatar ganin ya jagoranci shirin shiga tsakanin da nufin samar da mafita a rikicin wanda ke kara tsananta, bayan da Iran ta fara kara yawan sinadaran Uranium din ta da nufin karfafa sashen ta na makamin nukiliya a bangare guda kuyma Amurka ke ci gaba da yi mata barazanar fuskantar sabbin takunkumai.

A jiya Talata ne dai, shugaba Macron ya aike da karin tawaga ta 2 cikin wata guda zuwa Tehran don lallamar gwamnatin Iran wajen ganin ta ajje shirinta na yiwa yarjejniyar nukiliyar 2015 karan tsaye, wadda ta kayyade yawan sinadaran uranium din da kasar ke tacewa.

Tun bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliyar ta Iran a watan Mayun 2018, Iran ta fara fuskantar takun saka da Amurka tare da mayar mata da wasu takunkumai, matakin da ya tilastawa Iran fara karya ka’idojin da yarjejeniyar ta kunsa ta hanyar kara yawan sinadaran Uranium din da at ke tacewa zuwa kashi 5.

Cikin kalaman da shugaba Macron ya aikewa Iran ya bukaci Tehran ta kai zuciya nesa yayinda ya sha alwashin cewa EU za ta dauki matakin lallamar bangarorin biyu wajen ganin Amurka ta janye takunkuman a banagre guda kuma Iran ta dakatar da shirinta.

Ko a bara, Emmanuel Macron ya yi yunkurin ziyarar Tehran duk dai a yunkurin ganin kasar ba ta dauki matakin bijirewa yarjejeniyar ba, matakin da zai mayar da shi shugaban Faransa na farko da ya ziyarci Iran tun bayan 1976, sai dai batutuwa masu alaka da zargin yiwa yarjejeniyar zagon kasa dama rawar da kasar ke takawa a Syria ya tilasta shi dakatar da ziyarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.