Isa ga babban shafi
Iran-Turai

Iran ta zarce adadin Uranium da ta ke tacewa

A yau littinin kasar Iran ta wuce adadin da aka kulla da ita game da samar da makamashin Uranium karkashin yarjejeniyar shekara ta 2015.

Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani REUTERS/Abdullah Dhiaa Al-Deen
Talla

Wannan mataki na zuwa ne bayan sama da shekara daya, da Amurka ta janyen kanta daga cikin yarjejeniyar da aka kulla da kasar Iran da manyan kasashen na duniya

Wannan a cewar kasar Iran ta yi hakurin da ya wuce kima, kuma ta ga cewa sauran kasashen Turai da aka kulla yarjejeniyar tare, sun ki cewa uffa game da lamarin.

Kakakkin Hukumar makamashin na kasar Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce a yau Iran ta wuce adadin kashi 4.5, wanda ya wadata bukatun samar da hasken wutan lantarkin kasar tasu.

Kungiyar Tarayar Turai dai ta bayyana damuwa matuka inda ta yi kira ga Iran da ta sake shawara.

Kasashen Faransa, Jamus da Birtaniya dai wadanda ke cikin yarjejeniyar da aka kulla da Iran , tun lahadi suke neman Iran ta mutunta yarjejeniyar da aka kulla da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.