Isa ga babban shafi
Najeriya

Iran ta fara karya ka'idojin yarjejeniyar nukiliyarta

Hukumar Yaki da Yaduwar Makamin Nukiliya ta IAEA ta tabbatar cewar kasar Iran ta zarce adadin da aka gindaya mata na tace sinadarin Uranium a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka kulla da ita a shekarar 2015.

Shugaban Iran Hassan Rohani a cibiyar makamashin nukiliyar kasar
Shugaban Iran Hassan Rohani a cibiyar makamashin nukiliyar kasar Iranian Presidency / AFP
Talla

Mai magana da yawun hukumar  IAEA ya ce, binciken da hukumar ta gudanar, ya nuna cewar Iran ta zarce kilogram 300 na sinadarin wanda ya saba ka’ida.

Shi ma Ministan Harkokin Wajen Iran Javad Zarif ya tabbatar da zarce adadi tace makamashin na Uranium a daidai lokacin da kasar ke barazanar watsi da yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a ranar 7 ga wannan wata na Yuli saboda takunkumin da Amurka ke ci gaba da kakaba mata.

Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bukaci Iran da ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar.

A bangare guda, kasar Isra’ila ta bukaci daukacin kasashen Turai da su kakaba wa Iran takunkumi, yayinda Rasha ke cewa, Iran ta karya ka’idar ce saboda matsin lambar da take fuskanta daga Amurka .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.