Isa ga babban shafi
Iran-Turai

Iran ta yi watsi da shawarar manyan kasashe kan nukiliya

Iran ta yi watsi da kiraye-kirayen da manyan kasashen duniya suka yi mata na yin biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla da ita a shekarar ta 2015 na takaita adadin makamashin Uranium da take yi.

Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani HO / IRANIAN PRESIDENCY / AFP
Talla

 

Ita dai kasar Iran ta kafe ne da matsayinta na ranar 8 ga watan 5 cewa, zata yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla da ita saboda yadda shugaban Amurka Donald Trump ya kara kirba mata takunkumin karairaya ta, bayan da shi ma Trump ya janye daga yarjejeniyar tun a bara.

Tun jiya shugaban Iran Hassan Rouhani yace matakin su ya biyo bayan rashin cika alkawari ne da aka nuna masu, gashi kuma an gaza yin komi dangane da takunkumin da Amurkan ta malkaya mata.

Adadin makamashin Nukiliyan da aka bari Iran ta mallaka dai zai bata damar samarda hasken wutan lantarki, wanda ba a taba kai adadin bukatar samar da nukiliya ba.

Kasar Faransa dai ta fito fili ta gargadi Iran da cewa ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar, saboda babu wani alfanu idan ta fice.

A cewar Shugaban Iran idan har aka bukaci Amurka ta janye takunkumin da ta malkaya mata, to shakka babu Iran zata sauya matsayin data dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.