Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

May ta gana da shugabannin EU bayan nasara a kuri'ar yankan kauna

Firaministar Birtaniya Theresa da ta sha da kyar a kuri’ar yankan kaunar da ‘yan majalisa jam’iyyar ta suka kada mata a yammacin jiya, yanzu haka ta na wata ganawa da shugabannin kungiyar Tarayyar Turai a wani mataki da ta ke fatan cimma muradun majalisar gabanin kada kuri’a a sabuwar shekara game da shirin ficewar.

Theresa May cikin jawaban neman goyon baya da ta gabatar gaban zaman majalisar Tarayyar ta Turai ta jaddada kudurinta na sauka daga mulki gabanin zaben 2022.
Theresa May cikin jawaban neman goyon baya da ta gabatar gaban zaman majalisar Tarayyar ta Turai ta jaddada kudurinta na sauka daga mulki gabanin zaben 2022. REUTERS/Yves Herman
Talla

Yanzu haka dai May na ganawa da shugaban EU Donald Tusk gabanin ta kunkari takwarorinta na kasashe 27 da ke kungiyar a taron wanda ke zuwa kasa da makonni 3 bayan amincewa da shirin ficewar Birtaniyar daga EU.

Cikin bayanan da ta gabatar, Theresa May ta jaddada aniyarta na sauka daga mulki gabanin zaben Birtaniya na 2022 a dai dai lokacin da Majalisar ta sanar da kara lokacin kada kuri’arta kan kudirin na May zuwa nan da tsakiyar watan Janairu mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.