Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Majalisar Birtaniya za ta kadawa Theresa May kuri'ar yankan kauna

'Yan Jam’iyyar Konzabatib ta Firaminista Theresa May 48 ne su ka rubuta wasikar ganin sun sauya shugabancin Jam’iyyar su wadda za ta bada damar sauke May daga shugabancin kasar.Wannan mataki zai kai ga jefa kuri’a yau da yamma wanda zai yanke hukunci kan makomar Firaministar da ke fuskantar kalubale na cigaba da zama a kujerar ta ko kuma a’a.

Kuri'ar dai wadda za a kada kowanne lokaci a yammacin yau Laraba za ta fayyace makomar kujerar Firaministar.
Kuri'ar dai wadda za a kada kowanne lokaci a yammacin yau Laraba za ta fayyace makomar kujerar Firaministar. HO / AFP / PRU
Talla

Bisa ka’ida Yan Majalisu 48 wanda ke zama kashi 15 ke da hurumin kiran kuri’ar yankar kauna a zauran Majalisa ke gabatar da wasikar kuma shugaban masu rinjaye Graham Bradly ya ce tun jiya talata sun samu wannan adadi.

Yanzu haka ana can ana tafka mahawara kan makomar kasar da kuma shirin ficewa daga kungiyar kasashen Turai.

Kafin fara mahawarar Firaminista Theresa May ta yi tsokaci dangane da  bukatar sauya shugabancin inda ta ke cewa matakin zai jefa makomar Birtaniya cikin hadari, baya ga jefa al'umma cikin shakku la'akari da cewa ba za’a samu sabon shugaba nan da ranar 21 ga watan Janairu da aka gindaya a hukumance ba.

A cewar May sauya shugabanci zai kai ga mika tattaunawar ficewar ga ’yan adawar da ke Majalisa, haka zalika a cewarta sabon shugaban da za’a zaba bai zai samu damar kulla yarjejeniya ba, wanda har ta kai ga  bai wa majalisa damar amincewa da shi nan da ranar 29 ga watan Maris, lokacin da ya kamata kasar ta kammala ficewa daga EU.

Sai dai jagoran 'yan adawa Jeremy Corbyn da ya bukaci kammala mahawar domin kada kuri’a kan shirin ficewar daga EU, ya ce kasancewar May ta gaza cimma matsaya su kam za su kammala kada kuri'a kan shirin gabanin tafiya hutun kirsimeti.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.