Isa ga babban shafi
Birtaniya

May ta tsallake yunkurin 'yan majalisa na tsige ta

Fira Ministar Birtaniya Theresa May, ta lashe zaben da ‘yan majalisar jam’iyyarta suka jefa, don neman sauke ta daga matsayinta.

Fira Ministar Birtaniya Theresa May, a zauren majalisar kasar.
Fira Ministar Birtaniya Theresa May, a zauren majalisar kasar. HO / AFP / PRU
Talla

May ta lashe zaben yankan kaunar da kuri’un ‘yan majalisa 200 da suka yi na’am ta ci gaba da mulkinta, yayinda wasu 117 suka kada kuri’ar rashin amincewarsu da shugabancinta.

A karkashin dokokin tsarin zaben yankar kaunar dai dole ne sai Fira Minista Theresa May ta samu kuri’u 159 daga cikin kuri’u 317 kafin ta ci gaba da jagoranci.

Zalika a tsarin dokar Birtaniya, nasarar da May ta samu, ta tabbatar da cewa, daga .yan majalisar jam’iyyarta ba su da hurumin sake yunkurin sauke ta sai bayan shekara daya.

A cikin wata fira da ta yi ga kafofin watsa labarai, May ta bayyana cewa, za ta jajirce, domin ta kare matsayinta, wanda zai bata damar karasa aikin tabbatar da kammala ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar kasashen turai a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.