Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ta bukaci bayyanar matan da aka ci zarafinsu

Hukumomin Kasar Faransa sun bukaci matan da suka yi korafin cewa anci zarafin su lokacin bukukuwan samun nasarar gasar cin kofin duniya da kasar tayi, da su gabatar da kan su domin bi musu kadi.

Dubban mutane a Champs-Elysees da ke birnin Paris, yayin bukukuwan murnar samun nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, da Faransa ta yi.
Dubban mutane a Champs-Elysees da ke birnin Paris, yayin bukukuwan murnar samun nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, da Faransa ta yi. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shugaban ‘yan sandan Paris da Ministan kula da daidaito tsakanin jinsi suka bukaci matan su gabatar da kan su.

Mata da dama ne dai a kasar ta Faransa suka wallafa a shafin sada zumanta na twitter, cewar wasu maza sun sumbacesu da karfin tsiya, a daren da tawagar kwallon kafar kasar tayi nasara kan Croatia a wasan karshe da ta lashe kofi a Rasha, yayin da dubban magoya baya suka fansama kan titunan birnin Paris da wasu birane.

Wasu daga cikin matan sun bayyana cewa anyi lalata da su, a wasu wasannin da Faransa tayi nasara a lokacin gasar ta neman cin kofin duniyar, kafin ma a kai ga wasan karshe, harma yayin bukukuwar da aka gudanar yayin dawowar tawagar ‘yan kollan daga Rasha, a dandalin Champs Elysees, a nan ma matan sunce anci zarafinsu.

A cewar masu rajin kare hakkin bil’adama a kasar Faransa, mata na fuskantar barazanar fyade a kusan duk wasu manyan bukukuwa a kasar, ko yayin shagulgula da ake gudanar wa a tituna, musamman ma idan akan samu barasa cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.