Isa ga babban shafi
Faransa

Haramta Burkini ya janyo Muhawara a Republican

Batun haramta amfani da Burkini a wuraren shakatawa da ke gabar teku na ci gaba da janyo muhawara musamman tsakanin manyan ‘yan takara da ke neman shugabancin Faransa a bangaren Jam’iyyar Republican.

Batun haramta amfani da Burkini ya janyo muhawara a Faransa
Batun haramta amfani da Burkini ya janyo muhawara a Faransa REUTERS/Stringer
Talla

Tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy da kuma babban mai hamayya da shi a bangaren Jam’iyyar Republican a takarar shugabancin Faransa a zabe mai zuwa. Sun yi hannun riga ga batun haramta dokar Burkini wato sanya tufafi da ke nuna addinin wani a gabar teku wajen shakatawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata kotu ta dakatar da dage haramcin dokar Burkini. Yayin da kuma wani magajin gari a Faransa ya ce za su bijerewa hukuncin na kotun.

Sarkozy dai na goyon bayan dakatar da dokar yana mai cewa Faransa bata bukatar abin da zai nuna wasu alamun tana dogaro da wani addini.

Sai dai Allen Juppe yace hada kan al’umma shi ne muradin shi amma ba raba kanun faransawa ba.

Biranen Faransa da dama ne dai musamman a kudancin kasar suka haramta sa Burkini saboda barazanar hare haren ta’adanci.

Batun Burkini dai ya janyo muhawara tun hotunan da aka yada na wasu ‘yan sanda da aka nuna sun tursasawa wata mata cire mayafinta a gabar teku da kuma hoton bidiyo da ya nuna wani mai gidan abinci ya wulakanta wasu mata musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.