Isa ga babban shafi
Jamus-Faransa

An fara yunkurin hana sanya Burqa

Ministan cikin gida na kasar Jamus, ya bada da shawarar kafa dokar da zata hana matan musulmi sanya Burqa, daidai lokacin da ake mahawara dangane da sanya hijabi sakamakon hare-haren ta’addancin da ake kai wa a kasar. 

Ana muhawara kan sa Burqa a Jamus
Ana muhawara kan sa Burqa a Jamus Reuters
Talla

Ministan Jamus Thomas de Maiziere shi ne ya gabatar da wannan shawara kuma hakan na zuwa yayin da shugabar Jamus din Angela Merkel ke kokarin kwantar da hankulan al’ummar kasar saboda damuwa da yawan baki da ke shigowa kasar.

De Maiziere, wanda ya gana da wasu manyan ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau, ya ce yana son a haramta sanya Burqa ko kuma niqabi ne a wasu muhimman wurare da suka hada da ofisoshin gwamnati, makarantu, a cikin kotu da kuma sauran wuraren da jama’a ke taruwa.

Ministan dai ya ce sanya nikabi abu ne da ya yi hannun riga da al’udun Jamusawa, saboda haka bai kamata a bar mata na fitowa da shi bainar jama’a ba.

Yanzu haka dai wasu birane a kasar Faransa mai makotaka da Jamus sun fara daukar irin wannan mataki domin hanawa matan musulmi sanya tufafin da zai rufe jikinsu yayin linkaya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.