Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel ta ki sauya matsayinta kan baki a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi watsi da kira-kirayen janye matsayinta game da bakin haure samakon hare-haren baya-bayan nan da kasar ta fuskanta.  

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Shugabar ta ce, masu kaddamar da farmaki a kasar na bukatar haifar da cikas ne dangane da mu’amalarsu da al’umma da kuma kokarinsu na taimaka wa jama’a, abinda shugabar ta ce, sam ba zai yiwu ba.

Uwargida Merkel wadda ta katse ziyarar da ta shirya kai wa arewacin Berlin, ta fuskanci kafafan yada labarai a yau, inda ta shaida musu cewa, hare-haren ta’addanci har guda hudu da kasar ta gamu da su a cikin mako guda, na da matukar tayar da hankali amma ko kadan hakan bai razana mahukuntan kasar ba.

Shugabar dai ta jaddada matsayin da ta dauka a bara, lokacin da ta bude kan iyakar kasar don bai wa ‘yan gudun hijira kusan miliyan 1 da dubu 100 mafaka yawancinsu daga Syria, inda ta ce, har yanzu ta gamsu cewa za su kai ga gaci a manufufinsu.

Merkel ta ce uku daga cikin maharan na baya-bayan nan ‘yan gudun hijira ne yayin da kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da guda biyu daga ciki.

A karon farko kenan da Angela Merkel ta gabatar da jawabi a taron manema labarai tun bayan hare-haren wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.