Isa ga babban shafi
Jamus

Dan gudun hijira ya sake kai hari a Jamus

Hukumomin Jamus sun ce, wani dan gudun hijirar Syria ya dana bam a  wani gidan rawa da ke yankin kudancin  kasar, inda ya kashe kansa tare da raunana mutane da dama.

Jamus ta fuskanci hare-hare guda uku cikin mako guda
Jamus ta fuskanci hare-hare guda uku cikin mako guda Fuente: Reuters.
Talla

Wanna dai shi ne hari na uku da aka kai Bavaria a cikin mako guda.

Ministan cikin gidan kasar Joachim Herrmann ya ce, matashin mai shekaru 27 ya kai harin ne a gidan rawar kuma kusa da taron jama'ar da ke bikin kade-kade da raye-raye a garin Ansbach.

Ministan ya ce maharin ya shekara biyu a garin amma bai samu takardar shaidar zama ba, kuma lokacin da ya nemi shiga gidan rawar sai aka hana shi saboda ba shi da tikiti.

Wannan na zuwa ne bayan wani harin bindiga da aka kai birnin Munich wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9.

A makon jiya, Ministan cikin gida Herrmann ya gargadi al’ummar kasar cewar, su yi shirin ci gaba da fuskantar ire-iren wadannan hare-haren a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.