Isa ga babban shafi
Italiya

Jam'iyya mai ra'ayin kyamar baki ce kan gaba a zaben Italiya

Bangarorin Jam’iyya mai ra’ayin kyamar bakin haure a Italiya da kuma Jam’iyyar Five Star Movement na ikirarin nasara a zaben kasar da ya gudana a karshen makon daya gabata. Ikirarin nasarar Jam’iyyun biyu dai na zuwa a dai dai lokacin da ake gab da kammala kirga kuri’un da aka kada a zaben.

Ana saran dai jam’iyyar ta M5S ka iya samun kujeru 231 a karamar majalisar dokoki ta kuma samu kujeru 115 a babbar majalisar dokoki.
Ana saran dai jam’iyyar ta M5S ka iya samun kujeru 231 a karamar majalisar dokoki ta kuma samu kujeru 115 a babbar majalisar dokoki. REUTERS/Yara Nardi
Talla

Yanzu haka dai Jam’iyya mai ra’ayin kyamar bakin haure karkashin Matteo Salvini na da kaso 37 na ilahirin kuri’un da aka kada, yayinda ake ci gaba da kirge.

Tuni dai Salvini ya fara shirye-shiryen jan ragamar kasar mai yawan jama’a fiye da miliyan sittin bayan gagarumar tazarar da ke tsakaninsa da jam’iyyar shugaba Silvio Berlusconi Forza wadda yanzu haka ta ke da kuri’u kashi 14 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Wani taron manema labarai da Salvini ya kira ya ce lokaci ne da al’umar kasar za su ga sauyi ta hanyar kawo karshen barazanar tsaron da kasar ke fuskanta, musamman ta hanyar kwararowar bakin haure da kuma fitar da kasar da ga kungiyoyin hadaka.

To sai dai a bangare guda itama jam’iyyar M5S na can na makamancin ikirarin nasarar yayinda ta ke shirye-shiryen karbar shugabancin kasar.

Ana saran dai jam’iyyar ta M5S ka iya samun kujeru 231 a karamar majalisar dokoki ta kuma samu kujeru 115 a babbar majalisar dokoki.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus angela Merkel ta yi fatan kasar ta kammala kafa gwamnatin hadaka ba tare da daukar lokaci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.