Isa ga babban shafi
Italiya

Dan bindiga ya hallaka bakin haure a Italiya

‘Yan sandan Italiya sun tsare da wani dan bindiga da ya bude wuta kan wasu bakin-haure ‘yan nahiyar Afrika.

Mutane sun yi dandazo a wurin da dan bindiga ya raunata wani dan gudun hijira daga nahiyar Afrika a birnin Macerata, da ke Italiya.
Mutane sun yi dandazo a wurin da dan bindiga ya raunata wani dan gudun hijira daga nahiyar Afrika a birnin Macerata, da ke Italiya. REUTERS/Stringer
Talla

Matashin mai suna Luca Traini ya na rataye da tutar kasar Italiya a lokacin da ya hallaka bakin-haure 6 da kuma jikkata wasu da dama a garin Macerata.

Lamarin ya auku ne kwanaki kadan bayan da jami’an tsaron Italiya suka kame wani dan Najeriya da aka zargi da kashe wata matsahiya ‘yar kasar, tare da gididdiba namanta zuwa wasu jakunkuna, wadanda aka gano a gaf da garin na Macerata.

Bincike ya tabbatar da cewa Traini na da ra’ayin nuna wariya, zalika yana daga cikin masu adawa da shirin gwamnatin Italiya na bai wa bakin haure mafaka.

A ranar 4 ga watan Maris mai zuwa, za’a gudanar da zaben kasar, kuma batun goyon baya ko akasin haka akan sha'anin da ya shafi karbar ‘yan gudun hijira ko bakin haure, na daga cikin batutuwa masu muhimmanci da al’ummar kasar zasu mayar da hankali a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.