Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Le Pen zai zama bala'i ga Faransawa- Araud

Jakaden Faransa a Amurka Gerard Araud ya ce, zaben Marine Le Pen ta jam’iyar masu tsattsauran ra’ayi zai kasance babban bala’i ga Faransawa da Turai ba ki daya.

Marine Le Pen da ke neman kujerar shugabancin Faransa
Marine Le Pen da ke neman kujerar shugabancin Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Jakaden ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke nuna goyon bayansa ga kallaman takwaransa na Japan kan Le Pen da ke fatan lashe kujera shugabancin Faransa.

Le pen da ke adawa da karbar baki a Turai na fatan kafa tarihin bazata irin na zaben Amurka da ya bai wa Donald Trump nasara a Nuwamban bara.

Sai dai Mr. Araud ya shaidawa Jaridar Washington Post a lokacin wata hira cewa, nasarar Le pen babban bala’I ne, domin nasarar Le Pen da ke kokarin zama shugaba don janye Faransa daga kungiyar kasashen Turai, za ta ruguza kungiyar baki daya kamar yadda ya fadi, kuma ya kara da cewa, rashin Faransa a EU zai rage wa kungiyar tagomashi.

Sannan kuma daga wannan lokaci za a samu rugujewar kudin Euro tare da fadawa cikin matsalar tattalin arziki da za ta yi tasiri a duniya baki daya a cewar jakadan.

Jaridar Post dai ta bayyana Araud mai shekaru 64 a matsayin wanda ake mutuntawa a ayyukansa, sakamakon tsawon shekarun da ya dauka yana fafutuka.

A ranaku 23 ga watan Afrilu da 7 ga watan Mayu za a kada kuri'ar zabe a Faransa, yayin da wasu manyan jami’an diflomasiyar kasar ke barazanar ajiye aikinsu muddin Le Pen ta yi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.