Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa 50,000 na son Obama a matsayin Shugabansu

Yanzu haka Faransawa kusan 50,000 suka sanya hannu kan wata takarda da ke bukatar ganin tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tsaya takarar shugaban Faransa da za a yi a watan gobe.

Faransawa na son Obama a matsayin shugaban kasarsu
Faransawa na son Obama a matsayin shugaban kasarsu france24
Talla

Rahotanni sun ce akalla mutane sama da 48,000 suka sanya hannu kan takardar bukatar, saboda gajiyar da suka yi da shugabanin siyasar kasar.

Daya daga cikin masu shirya sanya hannun, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, sun gamsu da irin shugabancin Obama kuma ganin gazawar ‘yan siyasar kasar ya sa suke neman ya je ya tsaya takara.

Jami’in ya ce suna bukatar sanya hannun mutane miliyan guda don kai bukatarsu ga Majalisar kasa domin amincewa da ita.

Sai dai kalubalen Faransawan shi ne Obama ba dan kasar ba ne, abin da wasu ke danganta bukatar kamar wasa ko almara.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a dai ya nuna Marine Le Pen ‘yar jam’iyyar masu kishin kasa da ke adawa da baki za ta kai labara a zageye na farko tsakaninta da Emmanuel Macron da Francois Fillon da ke fuskantar Baraka a yakin neman zabensa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.