Isa ga babban shafi
Faransa

Ba zan tsaya takara ba- Juppe

Tsohon Firaministan Faransa Alain Juppe ya ce ba zai sake neman tsayawa takara ba domin maye gurbin Francios Filllon da ke fuskantar matsin lamba sakamakon zargin ya bai wa iyalansa aiki ba tare da ya bin ka’ida ba.

Tsohon Firaministan Faransa Alain Juppé
Tsohon Firaministan Faransa Alain Juppé GEORGES GOBET / AFP
Talla

Ana dai ganin Juppe ya dauki matakin ne domin hada kan Jam’iyyarsu ta Republican a yayin da zaben shugaban kasa ke karatowa.

Matakin da Alain Juppe ya dauka na kin sake tsayawa Takara, ya dada kwarin guiwa ga Francois Fillon da ke fuskantar baraka a yakin neman zaben shi.

Juppe wanda tssohon Firaminista ne a Faransa, ya tabbatarwa manema labarai a Bordeaux cewa bai zama dan takarar shugaban kasa ba a Republican.

Fillon ne dai ya doke Juppe a zaben fitar da dan takara a Jam’iyyar republican a watan nuwamba, amma badakalar da aka bankado akan Fillon ya dauki matar shi da yayan shi aiki a majalisa, ya sa wasu ke kiran ya janye takararsa ya ba Juppe.

Juppe ya shaidawa manema labarai cewa tun lokacin da sakamkon zaben fitar da gwnai ya nuna bai yi nasara ba ya yanke shawarar marawa Fillon baya.

Sai dai kuma yanzu babbar barakar da Fillon ke fuskanta shi ne yadda wasu ‘yan jam’iyyarsa ta Republican suka juya masa baya ciki har da jami’an yakin neman zaben shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.