Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu ta yanke hukunci dauri kan Jerome Cahuzac

Wata kotun a kasar Faransa ta zartar da hukuncin daurin gidan yari na tsawon shekaru Uku ga tsohon ministan kasafin kudin kasar, Jérôme Cahuzac, kan laifin gujewa biyan haraji tare da hallata kudaden haramu, a badakala mafi muni da aka bankado a wa’adin Shugaba Francois Hollande.

Tsohon ministan kasafin kudin Faransa Jérôme Cahuzac zai fuskanci hukuncin dauri
Tsohon ministan kasafin kudin Faransa Jérôme Cahuzac zai fuskanci hukuncin dauri REUTERS/Philippe Wojazer TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Shugaban kotun, Peimane Galeh-Marzban ne ya sanar da Jérôme Cahuzac, hukunci da aka zartar masa, tare da matsayin laifin gujewa biyan haraji da zama daya daga cikin manyan laifukan da ke ruguza tsarin zaman al’umma, inda ya ce Cahuzac ya share tsawon shekaru yana gujewa biyan haraji da gangan.

Shekaru 4 bayan bankado badakalar, Jérôme Cahuzac, bai zama shi ka dai aka yankewa hukunci ba, harda Tsohuwar matarsa Patricia Menard wace a wani yanayi na cin amana ta fallasawa masu shara’a asusun ajiyar banki da ke tsibirin Man kasar Britaniya.

Har ma a lokacin da yake rike da mukamin ministan kasafin kudi a 2012, bai sa ya kawo karshen wannan dabi’a ba, duk da cewa shi ya kamata ya bada misali tare da tabbatar da tsayuwar yaki da mummunar dabi’ar ta kin biyan haraji a kasar.

Tuni dai lauyoyin da ke kare shi, suka bayyana aniyar daukaka kara a kan wannan hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.