Isa ga babban shafi
Faransa-Morocco

Hollande yace zai yi wuya tsohon ministan kudinsa Jerome Cahuzac ya samu ahuwa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yaba da matakan ci gaban Demokradiya da gwamnatin kasar Moroco ta dauka, a lokacin da shugaban ke ziyara a kasar, amma badakalar haraji da ta shafi Ministansa kudinsa Jerome Cahuzac ta shafe labarin ziyarar shugaban.

shugaba François Hollande a gaban taron maneman labarai a Rabat,  4 avril 2013.
shugaba François Hollande a gaban taron maneman labarai a Rabat, 4 avril 2013. REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Shugaba Hollande yace, a kullum kasar Morocco na daukar matakan ci gaban Demokradiya, yana mai yabawa da sabon kundin tsarin mulki da Sarki Muhammad na Shida ya samar sakamakon zangar zangar kin jinin gwamnatocin kasashen larabawa da ta yi awon gaba da wasu shugabanni.

Ziyarar shugaba Hollande a morocco na zuwa ne a dai dai lokacin tsohon Ministan kudin shi Jerome Cahuzac ke fuskantar tuhuma wanda kuma ya fito fili ya amsa yana da kudaden ajiya a bankunan Switzerland don kada ya biya haraji

Masu sharhi dai suna ganin wannan kamar Tsunami ce ta shafi siyasar Faransa, inda kowa ya zira ido yaji jawabin shugaba Hollande game da wannan badakala bayan ya kammala ziyara a moroco

Hollande dai ya yi Allah waddai da Cahuzac yana mai cewa ya aikata laifin da yana da wahala ya samu afuwa, tare da musanta yana da masaniya game da asusun sirrrin Cahuzac

Yanzu haka dai shugaba Hollande ya sha alwashin kaddamar da sabuwar doka da za ta bayar da damar gudanar da binciken dukiyar ministoci da ‘Yan majalisu.

Labarin badakalar Cahuzac ne dai, ya shafe labarin ziyarar Hollande a Morocco wanda masana suka bayyana a matsayin rikicin siyasa mafi muni tun lokacin da shugaban ya karbi mulki a watan mayun bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.