Isa ga babban shafi
Faransa

Ministan kasafin kudin Faransa, Cahuzac ya ajiye aikinsa

Ministan tsara kasafin kudin kasar Faransa Jerome Cahuzac ya sauka daga mukaminsa, bayan da masu gabatar da kara suka bayyana binciken da suka yi ga wani asusun ajiya na asiri da Ministan ya yi amfani da shi ya na boye wasu kudade a kasar Swizland.

Ministan Kasafin Kudin Faransa, Jerome Cahuzac
Ministan Kasafin Kudin Faransa, Jerome Cahuzac
Talla

Masu gabatar da karar dai sun bayana wannan halin na Cahuzac a matsayin babban abin kunya ga jam’iyyar Socialist mai mulki a kasar.

Wanna murabus da Cahuzac ya yi, ya zo ne sa’oi kadan bayan masu gabatar da kara sun bayyana kaddamar da bincike game da zargin bayan wata kafar yada labarai ta fallasa cewa ya mallaki asusun.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.