Isa ga babban shafi
Faransa

Cece-kuce kan matsalar tsaro a Faransa

A Faransa yanzu haka ana ci gaba da sa-in-sa a game da zargin kin daukar matakai domin kare kasar daga hare-haren ta’addanci.

Ana zargin jami'an tsaro da yin sakaci a harin Nice na Faransa
Ana zargin jami'an tsaro da yin sakaci a harin Nice na Faransa REUTERS/Eric Gaillard
Talla

To sai dai Firaministan kasar Manuel Valls, karo na farko ya amince da cewa bangaren shari’a ya yi sakaci a game da wannan batu.
 

Zargin sakaci ta bangaren tsaro ya bijiro ne tun daga lokacin da wani mutum ya kashe mutane 84 ta hanyar taka su da mota a cikin wannan wata a garin Nice, lokacin da al’ummar kasar ke murnar zagayowar ranar dimokuradiyya.

To sai dai zargin ya sake bijirowa tare da samun goyon baya daga wasu manyan ‘yan siyasa na kasar, bayan da aka tabbatar da cewa daya daga cikin maharan da suka yanka shugaban wani coci a birnin Rouen na Normandie, kotu ce ta sallame shi duk da cewa cikakken dan ta’adda ne.
 

Karon farko Firaminista Valls ya amince bangaren shari’a ya yi sakaci, to sai dai ya ce daga ranar daya ga watan satumba mai zuwa, Faransa za ta bude wata cibiya ta musamman da za a rika tsare wadanda ake ganin cewa sun fara nuna halaye irin na masu da’awar jihadi a kasar.

Wasu ‘yan siyasa dai na ganin cewa gwmanatin Faransa ta gaza wajen bayar da kariya ga al’ummarta, lura da yawan hare-haren da aka kai daga watan Janairun bara zuwa wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.