Isa ga babban shafi
Faransa

An gano mutun na biyu a harin cocin Faransa

Masu shigar da kara na gwamnatin Faransa, sun bayyana Abdel Malik Petijean mai shekaru 19 a matsayin daya daga cikin mahara biyu da suka kashe limamin cocin kasar a ranar Talata.

Cocin da aka yi garkuwa da jama'a a Faransa
Cocin da aka yi garkuwa da jama'a a Faransa CHARLY TRIBALLEAU / AFP
Talla

Masu shigar da karar sun ce, shi ma Malik sananne ne ga jami’an tsaro tamkar maharin farko Adel Kermiche.

Jami’an tsaro sun yi nasarar harbe matasan guda biyu bayan sun yi garkuwa da masu ibada a cocin na Saint-Etienne, inda suka kashe limamin cocin, Jacque Hamel mai shekaru 86.

Kungiyar IS mai da’awar jihadi ta fitar da hoton bidiyo, inda ta ikirarin cewa, matasan sun yi mata mubaya’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.