Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa tayi allawadai da kisan limamin Mujami'a

Hukumomin Kasar Faransa na ci gaba da bayani kan wadanda suka kai hari suka kuma kashe daya daga cikin limaman kristocin kasar Fr Jacques Hamel mai shekaru 85 a Saint Etienne.

Shugaban Faransa Francois Hollande a Saint Etienne
Shugaban Faransa Francois Hollande a Saint Etienne REUTERS/Ian Langsdon/Pool
Talla

Babban mai gabatar da kara na kasar Francois Mollins ya bayyana daya daga cikin maharan a matsayin Adel Kermiche, matashi mai shekaru 19 wanda yayi kokarin zuwa kasar Syria amma bai samu nasara ba.

Mollins yace matashin yayi kokarin tafiya Syria a watan Maris na bara amma sai aka kama shi a Jamus, kuma lokacin da aka mayar da shi gida jami’an tsaro sun yi ta sa ido akan sa da kuma hana shi tafiya.

Jami’in yace bayan watanni biyu ya sake subucewa inda aka kama shi a kasar Turkiya.

Bayanai dai sun nuna cewa mutane biyu suka kai harin, inda suka yanka Fr Hamel.

Tuni shugaban kasar Faransa Francois Hollande yayi Allah wadai da kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.