Faransa
Kokarin sauya rahoton harin Nice na Faransa
Wata jami’ar 'yan sandan Nice da ke kasar Faransa ta zargi ministan cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve da kokarin tirsasa mata don sauya rahotan harin da aka kai birnin Nice wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 84.
Wallafawa ranar:
Talla
Sandra Bertin da ke kula da bangaren daukar hoto ta ce ministan ya bukace ta ta sauya rahotan hotan wurin da aka kai harin wanda zai nuna cewar 'yan sanda suna wurin alhali kuma hotan kamara bai nuna su ba.
Ministan wanda yake shan zargi kan rahsin daukar matakan hana aukuwar harin, ya yi barazanar kai Sandra gaban shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu