Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Awatan da ya gabata, kimanin bakin haure dubu 168 suka kutsakai a Turai

Sama da bakin haure 168,000 suka shiga nahiyar turai ta ketara tekun Mediterranie a watan satumbar da ya gabata, al’amarin da ya rubanya gida 5 na yawan yan bakin haure dasuka shiga nahiyar ta turai a daidai irin wannan lokaci a shekararda ta gabata

Bakin hauren na kutsa kai a nahiyar turai ta Teku
Bakin hauren na kutsa kai a nahiyar turai ta Teku REUTERS
Talla

Adai gefen kuma, garin Hambourg na kasar Jamhus ya bayyana aniyarsa na karbar wasu cibiyoyin kasuwanci da ba a amfani da su, domin tsugunar da dubban masu neman mafakar gudun hijira a kasar, idan har bukatar hakan ta taso, kamar yadda wata sanarwa da ofishin magajin garin birnin na Hambourg ta nunar

Kasar Jamus dai, na daya daga cikin kasashen turai da suka bayyana aniyarsu, ta karbar yan gudun hijirar kasar Syriya, dake ci gaba da kwararowa anahiyar turai, sakamakon yakin basasar sama da shekaru 4 da daidaita kasarta Syriya da kuma ya banzama miliyoyin al’ummar kasar hijirazuwakasashen ketare
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.