Isa ga babban shafi
EU

EU ta bayar da Euro biliyan daya domin taimakawa bakin haure

Shugabanin Kungiyar kasashen Turai sun amince su baiwa Majalisar Dinkin Duniya euro biliyan daya dan magance matsalolin da bakin dake kwarara zuwa nahiyar ke fuskanta.

Bakin haure a birnin Paris
Bakin haure a birnin Paris AFP/François Guilot
Talla

Sanarwar bayan taron da shugabanin suka yi ta nuna cewar za’a mika kudaden ne ga hukumar samar da abinci ta Majalisar da kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira.

Wannan dai na zuwa ne a wani lokaci da kasashen Afirka dake da wakilci a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya tare da Venezuela suka ki amincewa da bukatar Birtaniya na anfani da karfin soji kan masu safarar baki zuwa nahiyar Turai.

Birtaniya dai ta bukaci Majalisar da ta amince da shirin anfani da karfin soji wajen afkawa bakin da kuma kwace jiragen su a teku dan shawo kan matsalar da ta addabe su yanzu haka.

Bakin haure sama da dubu daya ne suka rasa rayukan su a wannan shekarar kawai a tekun Mediteranean a yayin da suke tserewa rikici a kasashen su zuwa Nahiyar Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.