Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

Tarayyar Turai ta dakatar da ba da tallafi ga Manoman yankin

Kungiyar tarayyar turai ta dakatar da tallafin Euro miliyan 125, da ta yi kudurin bayarwa ga manoman Nahiyar da suka yi hasarar kayayyakin gonakinsu sakamakon takunkuman karya tattalin arziki da aka kakabawa kasar Rasha, abinda kungiyar ta ce an samu rashin gaskiya daga bangaren manoman kasar Pologne da ke neman a biyasu diyar da ta wuce kima

poland-export.com
Talla

A watan da ya gabata ne dai kungiyar ta tarayyar turai ta bayyana daukar wasu jerin matakan gaggawa domin tallafawa manoman nahiyar da suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali dangane da takunkuman hana sayarwa Rasha kayayakin gona da kungiyar ta yi, bayan da ta zargi Rasha da tallafawa ‘yan tawayen kasar Ukraine.

Sai kuma a cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta tarayyar Turai, ta bayyan cewa, ta dakatar da bada wannan tallafi ga manoman, bayan da ta ce ta bankado rashin gaskiya ga masu neman biyasu diyar kayayyakin gonakinsu da suka ce sun lalace sakamakon takunkuman da aka kakabawa Rasha.

Kungiyar ta ce, ta dauki wannan mataki ne, bayan ganin kayyakin gonar da ake son a biya diya a kansu sun karu fiye da yawan kayayakin da ake fitarwa daga kasashen zuwa kasar Rasha a cikin wannan shekara.

Wata majiya daga kungiyar ta tarayar turai da bata yarda a bayyana sunanta ba ta ce, kungiyar na da matukar shakku kan sakamakon hasarar da manoman kasar Pologne suka gabatar, wanda tace tana bukatar gudanar da bincike tukuna, kamin daukar mataki na gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.