Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Abubuwan da ke cikin yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai wakilan kasar Kasar Ukraine, Rasha, Kungiyar tsaro ta nahiyar Turai da kuma ‘yan awaren Ukraine suka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin da ake fama da shi a gabashin Ukraine.

Gumurzu a wajen garin Marioupol da ke Ukraine.
Gumurzu a wajen garin Marioupol da ke Ukraine. REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

Wasu daga cikin batutuwan da ke kunshe a wannan daftari sun hada da gaggauta tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da ke yakar juna, yin musayar fursunonin yaki, janyewar ‘yan tawaye daga garuruwan da suka kama sannan da ficewar sojojin haya ko kuma ‘yan asalin kasashen waje da suka shiga cikin Ukraine domin taimaka wa wani bangare da ke da hannu a wannan rikici.

To sai dai kwana daya bayan kulla yarjejeniyar ne aka bayar da sanarwar cewa an yi musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu a wani wuri da ke kusa da iyakar Ukraine da Rasha.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.