Isa ga babban shafi
Ukraine

An tsagaita wuta a Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun ce yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince da ‘Yan tawayen Ukraine da suka mamaye gabacin kasar tana kan aiki bayan bangarorin da ke rikici a Ukraine sun zargi juna da karya yarjejeniyar.

Wani mazauni Marioupol a kusa da motar yaki a gabacin Ukraine.
Wani mazauni Marioupol a kusa da motar yaki a gabacin Ukraine. REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

‘Yan tawayen Ukraine da ke kishin Rasha da kuma Gwamnatin kasar dukkaninsu sun zargi juna da karya yarjejeniyar da Rasha ta tsara domin kawo karshen rikicin kasar na tsawon wata biyar da ‘Yan tawaye ke barazanar raba Ukraine gida biyu.

Wani Dan Majalisa Vladimir Makovich, a sabuwar gwamnatin Donestk ta ‘Yan tawaye, ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa dakarun gwamnatin Ukraine sun harba makamai masu linzami a wajen Donestk bayan yarjejeniyar ta fara aiki.

Yarjejeniyar dai ta matakai 12 da bangarorin biyu suka amince a Belarus ita ce ta farko tun lokacin da ‘Yan tawaye suka mamaye gabacin Ukraine a watan Afrilu.

Bayan da Amurka da kasashen Yammaci suka amince su tsaurara wa Rasha Takunkimi saboda dari dari da suke yi da ita akan rikicin Ukraine, Gwamnatin Rasha tace zata mayar da martani

A ranar Litinin ne Amurka da Turai suka ce zasu sake karfafa Takunkumi ga Rasha amma zasu sassauta idan har Rasha ta janye dakarunta a gabacin Ukraine tare da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.