Nigeria
An rufe makarantu 85 a jihar Borno saboda Boko Haram
Rahotannin da ke fitowa daga Borno a arewacin Nigeria na nuna cewa hukumomin Jihar sun rufe makarantun sakandare 85, har sai illa masha Allahu.Hukumomin sun dauki wannan matakin ne saboda fargabar hare hare, daga kungiyar nan ta Boko Haram. Rufe makarantun 85 zai sa yara fiye da dubu 120 su ci gaba da zama a gida, a jihar da ke fama da tashe tashen hankula, tsawon shekaru 5.Ko a shekarar bara, sai da gwamnan jihar ta Borno, Kashim Shettima yace ‘yan bindigan sun kona fiye da azuzuwa 800, wasu har fiye da sau 2.
Wallafawa ranar: