Isa ga babban shafi
Najeriya

Dubban mutanen Najeriya sun tsere wa rikicin Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya tace dubun dubatar ‘yan gudun hijira ne suka tsere daga tashe tashen hankulan da ke faruwa a arewacin Najeriya zuwa kashen Nijar da Kamaru da ke makwabtaka da kasar.

Wata mata da 'Yayanta dauke da kayansu tana shirin yin kaura bayan harin da aka kai a garin Kawuri a Najeriya
Wata mata da 'Yayanta dauke da kayansu tana shirin yin kaura bayan harin da aka kai a garin Kawuri a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Hukumar da ke kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace, tashe tashen hankulan da ake yi sun tilastawa kimanin mutane dubu biyu tserewa zuwa kasar Nijar mai makwabta da Najeriya, a makonni hudu da suka gabata kawai.

Mai Magana da yawun hukumar Adrian Edwards yace ‘yan gudun hijirar da suka tsallaka zuwa yankin Difa na Jamahuriyar Nijar, da kuma kasashen Kamaru da Chad, suna bayar da labarin yadda ake cin zarafin bil Adama.

Yace ‘yan gudun hijirar suna bayar da labarin yadda ake wurga gawarwaki a cikin gidajen jama’a, wasu gawarwakin kuma suna yawo a kan ruwa, yayin da ake samun rahoton sace mata da kananan yara.

Hukumar tace ba a gane masu kitsa wadannan aika aikan sai dai ana dora alhakin hakan, ga Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnna Lil Da’ati Wal Jihad da ake kira Boko Haram, wadanda ake zargi sun kashe a kalla mutane 500, a cikin wannan shekara ta 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.