Najeriya: Mutane 37 aka kashe a harin Adamawa
Akalla mutane 37 suka mutu a hare haren da ‘Yan bindiga da ake kyautata zaton Mayakan Kungiyar Boko Haram ne suka kai a Jahar Adamawa, kamar yadda Jami’an gwamnati da mazauna garuruwan da aka kai hare haren suka tabbatar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban karamar hukumar Madagali a Jahar Adamawa, Maina Ularamu yace an kai jerin hare hare ne guda uku ne a Shuwa da Kirchinga da Michika.
“‘Yan bindigan sun raba kansu ne gida uku” kamar yadda ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa.
Ularamu yace a garin Shuwa mutane 25 ne aka kashe bayan an gano gawawwakin mutane takwas a wata makarantar mabiya Addinin Kirista.
Rahotanni sun ce dukkanin ‘Yan bindigan sun yi shiga ne sanye da kakin Soja a hare haren da suka kai.
Tun da farko dai, Jami’an tsaro sun tabbatar da hare haren da aka kai a Adamawa amma sun ce Soja guda ne aka kashe da wasu fararen hula guda uku.
Jahar Adamawa dai tana cikin Jahohi uku a yankin arewa maso gabaci da aka kafawa dokar ta-baci, kuma tun daga farkon shekara ta 2014 zuwa yanzu akalla mutane 300 suka mutu a hare haren da aka kai a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu