Sojin Najeriya sun ce sun kashe ‘Yan Boko Haram 20 a Mafa
Rundunar sojin Najeriya tace Sojojinta sun kashe Mayakan Boko Haram 20 a yankin Mafa a Jahar Borno wannan kuma na zuwa ne bayan Gwmanatin Tarayya ta rufe makarantu a yankin arewa maso gabaci domin kaucewa hare haren da ake kai wa dalibai.
Wallafawa ranar:
A cikin Sanarwar da Kakakin rundunar Sojin kasar Chris Olukolade ya fitar yace sun mamayi mayakan ne a harin kwantar bauna a ranar Laraba a yankin Mafa da ke cikin Jahar Borno.
“Mayaka Ashirin ne suka mutu” a cewar Olukolade a cikin sanarwar.
A ranar Lahadi akalla mutane 29 aka kashe a Mafa bayan wasu hare haren bama bamai guda biyu da aka kai a Maiduguri da ya yi sanadin mutuwar mutane 35 inda wani harin kuma ya yi sanadiyar mutane 39.
Sanarwar Sojin na Najeriya na zuwa ne bayan Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta bayar da umurnin rufe wasu makarantun Gwamnati a Jahohin Yobe da Adamawa da Borno.
Akalla mutane 45 suka mutu a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a wata Makarantar Sakandare ta gwamnati a Buni Yadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu