Isa ga babban shafi
EU-Tsakiyar Afrika

Kasashen Turai suna nazarin aikawa da Dakaru a Tsakiyar Afrika

Kungiyar tarayyar Turai na duba yiwuwar aikawa da dakarun hadin gwiwa zuwa Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, domin dakile rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, yayin da sama da mutune miliyan daya suka fice daga gidajensu.

Dakarun Sojin Faransa da na Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Dakarun Sojin Faransa da na Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika AFP / MIGUEL MEDINA
Talla

A ranar Juma’a mai zuwa ne ake sa ran kungiyar za ta tattauna wannan batun a taron da zata yi a Brussels, wanda zai ba da damar aikawa da dakarun domin su tallafawa na Faransa da na Afrika da yanzu haka ke kasar.

Wannan batu na zuwa ne kusan watanni biyu bayan da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya nemi taimakon kasashen nahiyar da su kawo mai dauki domin magance rikicin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

Amma wannan kiran na Shugaba Hollande bai sauya wani abu ba, inda kasashen Birtaniya da Belguim da kuma Jamus ne kawai suka taimaka da kayyakin aiki, amma a yanzu ana sa ran kungiyar zata dauki matsaya a ranar 20 ga wannan wata bayan taron da za ta yi a gobe Juma’a.

Rikicin na Jamhuriyar Tsakiyar Afrikan ya kashe mutane sama da dubu yayin da mutane sama da miliyan daya suka tserewa gidanjensu domin kaucewa rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.