Isa ga babban shafi
Chadi-Afrika ta Tsakiya

Chadi ta kira taro game da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Shugabannin kasashen Afrika na shirin fara wani taro a kasar Chadi a yau Alhamis domin tattauna makomar Shugaban kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika Michel Djotodia, a kokarin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a kasar bayan shafe makwanni ana rikici.

Shugaban kasar Chadi  Idriss Deby yana zantawa da Ministan tsaron Faransa  Jean-Yves Le Drian game da Jamhuriyar tsakiyar Afrika a Ofishin shugaban kasa.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby yana zantawa da Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian game da Jamhuriyar tsakiyar Afrika a Ofishin shugaban kasa. AFP/Brahim Adji
Talla

Babu dai wasu bayanai game da wannan taro da Shugaban kasar Chadi Idris Derby ya kira da zai kunshi shugabannin kungiyar kasashen tsakiyar Afrika ta CEEAC.

Ministan harakokin Wajen kasar Faransa Laurent Fabius, shi ne ya kyankyasa labarin za’a yi wannan taro a cikin wata hira da jaridar kasar Faransa Le Parisien.

Tun lokacin da Mayakan Saleka suka yi juyin mulki, kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika ta fada rikici inda Djotodia ya dare saman kujerar shugaban kasa bayan hambarar da François Bozize.

Alkalumman rikicin kasar sun ce sama da mutane 1,000 ne suka mutu yayin da daruruwan mutane suka gujewa gidajensu.

Wata majiya tace babbar Ajandar taron shugabannin kasashen na Afrika a Chadi ita ce neman Djotodia ya yi murabus domin samun zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.