Isa ga babban shafi
Najeriya-Afrika ta tsakiya

Najeriya ta fara kwaso mutanenta daga Afrika ta tsakiya

Kakakin Tsaro na Sojan Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade yace suna dukkan kokari domin tattaro mutanen kasar kimanin 1,620 da suka makale a kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, inda ake ta gwabza fada.

tashar jirgin sama a Birnin Bangui shake da mutane 'yan kasashe waje da ke shirin ficewa kasar Jamhuriyyar tsakiyar saboda rikici
tashar jirgin sama a Birnin Bangui shake da mutane 'yan kasashe waje da ke shirin ficewa kasar Jamhuriyyar tsakiyar saboda rikici EUTERS/Andreea Campeanu
Talla

A cewar Olukolade tun a ranar Juma’a ne aka fara kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Bangui.

Mazauna birnin Bangui na kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa, musamman baki wadanda har yanzu ba su tsere ba na ci gaba da nuna matukar damuwa game da halin da suke ciki.

Rahotanni sun ce a tsakiyar kasuwar Bangui wani ya jefa gurneti da ya jikkata mutane hudu, ciki akwai mata biyu, da wani sojan Afrika.

Tun a watan Maris ne kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika ta shiga rudani bayan Michel Djotodia ya jagoranci mayakan Seleka suka karbe mulkin kasar daga hannun François Bozize.

Akwai dakarun Faransa da na Afrika da ke kokarin wanzar da lafiya a kasar inda rahotanni suka ce sama da mutane 1,000 ne suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.