IMF
Hukumar ba da lamuni ta IMF ta yaba da matakin da Cyprus ta dauka
Shugabar Hukumar ba da lamuni ta Duniya, Christine Lagarde, ta yaba da yarjejeniyar da aka kulla da kasar ta Cyprus.
Wallafawa ranar:
Talla
Ta kuma yaba wa shugabanin Cyprus saboda matakan da suka dauka masu tsauri. Inda ta ce hakan shine zai magance matsalar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta
“Ina so in yabawa shugabanin Cyprus kan matakan da suka dauka masu tsauri dan ceto tattalin arzikin su, magance matsalar manyan bankunan kasar, da kuma mayar da ingancin ayyukan bankuna a kasar.” Inji Lagarde
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu