Birtaniya ta yi watsi da bukatar Hukumar Lamuni
Minsitan kudin kasar Birtaniya George Osborne, ya yi watsi da wani kira da Hukumar Lamuni ta duniya IMF ta yi, inda ta nemi Birtaniya ta sassauta shirin matakan tsuke bakin aljihun da ta dauka. Kamar yadda Babban Masanin tattalin arzikin hukumar IMF, Olivier Blanchard yace tattalin arzikin kasar Birtaniya kan iya fadawa cikin wani mummunan hali.
Wallafawa ranar:
Mista Oliviar yace yakamata kasafin kudin da Birtaniya za ta gabatar a watan Maris ya kasance a wani lokaci da za’a yi nazarin matakan da aka dauka a baya.
Sai dai Osborne ya fito ya ce, basu da shirin dakatar da matakan a yanzu, har sai sun cim ma wa’adin da aka diba, wanda zai kai har shekarar 2017 kamar yadda aka tanada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu