Birtaniya na iya ficewa Kungiyar Turai idan al’ummar kasar sun amince-Cameron
Firaministan Birtaniya David Cemeron ya yi alkawalin ba al’ummar kasar damar kada kuri’ar amincewa ko ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai idan Jam’iyyar shi ta lashe zabe. Wannan matakin kuma ya daga hankalin Faransa da Jamus.
Wallafawa ranar:
Sai dai Cameron yace zai yi kokarin sasanta huldar Bitaniya da kungiyar Turai kafin ya ba Al’ummar kasar damar kada kuri’a.
Mista Cameron yana nufin Birtaniya za ta fice daga kungiyar Tarayyar turai idan Al’ummar kasar sun amince ko kuma idan sun amince a koma teburin sasantawa.
Sai dai akwai gargadi da Faransa da Jamus suka gabatar wa Birtaniya game da wannan kudirin Yanzu haka kuma David Cemeron ya fara fuskantar suka daga Jam’iyyar adawa ta Labour wadanda suka ce alamun gazawa ne ga Firaministan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu