Isa ga babban shafi
Faransa

Zai yi wuya Birtaniya ta fice kungiyar EU, inji Fabius

A yau Laraba kasar Faransa ta bayyana yunkurin Firaministan kasar Birtaniya, David Cameron, na gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a, don duba zaman kasar a kungiyar taraiyyar Turai, a matsayin abu mai cike da hadari. Cikin hirar da ya yi da wani gidan radiyon kasar, Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya ce zai yi wuya Birtaniya ta iya ficewa daga kungiyar ta tarayyar Turai.  

Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Lokacin da yake mayar da martani ga kalaman Mista Cameron, da ya ce, zai sake tattauna matsayin Birtaniya a kungiyar, Fabius ya ce Faransa na matukar bukatar ganin Birtaniya ta taka rawa mai inganci cikin kungiyar, amma ba za ta amince da kasashe su rinka zaben irin tsare-tsaren da za su amince da su ba.
 

Ya kwatanta taraiyyar ta Turai, da kungiyar kwallon kafa, da ya ce da zaran dan wasa ya shiga, bashi da ikon ya ce shi wasan Rugby zai buga, bayan kwallon kafa ake bugawa.
 

Cameron ya yi alkawarin gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a, tsakanin shekarar 2015 da 2017, a bayan zaben kasar, da ba zai wuce 2015 ba, wannan za ta faru ne kawai, in har jam’iyyar shi ta Conservative ta ci gaba da rike madafun ikon kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.