Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Faransa da Jamus sun cika shekaru 50 da cim ma yarjejeniyar sulhunta kansu

Shugaban Faransa François Hollande da Angela Merkel ta Jamus sun gudanar da taro domin bukin cika shekaru 50 da cim ma yarjejeniyar sulhu a tsakanin kasashen biyu Bayan zargin dangantakar Faransa da Jamus ta samu rauni,

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

A lokacin da shugabannin ke ganawa sun ce akwai kauna mai karfi a tsakanin Faransa da Jamus

A shekarar 1963 ne tsohon Shugaban kasar Faransa Charles de Gaulle da takwaransa na Jamus Konrad Adenauer suka amince da yarjejejniyar sulhu domin kawo karshen gabar da ke tsakanin Faransa da Jamus bayan kawo karshen yakin Duniya na Biyu.

Bukin cika shekarun 50 tsakanin kasashen biyu na zuwa ne bayan zargin dangantakar kasashen biyu na sukurkucewa saboda sabanin dubarun warware matsalar tattalin arziki da ke addabar wasu kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.