Isa ga babban shafi
IMF-Masar

Gwamnatin Masar da IMF sun sake komawa Teburin tattaunawa akan bashi

Kasar Masar da Hukumar bada lamuni ta IMF, sun koma teburin tattaunawa akan wani bashi da kasar ta Masar ke bukata daga hukumar IMF domin samun damar gudanar da ayyukanta na yau da kullum a kasar.

Shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi a lokacin da yake ganawa da Shugabar hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF
Shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi a lokacin da yake ganawa da Shugabar hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF Reuters
Talla

Kakakin IMF, Wafa Amr, ta bayyanawa manema labarai cewa sabuwar gwamnatin kasar tMasar sun fara tattaunawa da hukumar IMF akan yadda za a bada bashin.

Tuni kuma mai magana da yawun, gwamnatin shugaba Muhammed Morsi, Yaseer Ali Said shi ma ya bayyana cewa sun mika tsare- tsaren habaka tattalin arzikin kasar ga hukumar IMF.

Hukumar IMF ta umurci gwamnatin Masar ta bayar da tsare-tsaren ne, da kuma wasu hanyoyin samun kudadenta daga wasu hukumomi da kasashe domin hukumar ta tantance ko Masar ya dace a bata bashin, wanda ya kai kudi dalar Amurka Biliyan 4.8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.