Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Sandan Faransa sun kai samame a gidan Christine Lagarde

‘Yan sandan Faransa sun kaddamar da wani bincike a gidan Christine Lagarde shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF akan wata badakalar kudi a lokacin da tana Ministan Gwamnatin kasar.

Shugabar hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF, Christine Lagarde.
Shugabar hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF, Christine Lagarde. REUTERS/Pascal Lauener
Talla

Ana binciken Christine Lagarde ne game da tsoma baki a 2007 ga rikicin da ya shafi Bernard Tapie attajirin kasa da kuma bankin Lyonnais a kotu wanda hakan ya sa Tapie ya kwashi kudi euro miliyan 400.

Lauyan Lagarde Yves Repiquet ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP sun ba ‘Yan sanda hadin kai domin gudanar da binciken.

Tapie Attajiri ne kuma dan siyasa wanda ya taba rike mukamin minista a zamanin mulkin shugaba Francois Mitterand kafin daga baya ya koma yana goyon bayan Nicolas Sarkozy a zabukan 2007 da 2012.

An taba tura Tapie zuwa gidan yari bayan kama shi da laifin yin cogen wasa a lokacin da yana shugaban kungiyar Olympique Marseille.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.