Isa ga babban shafi
EU-Girka-IMF

Shugaban IMF Lagarde ta yaba hanyoyin warware rikicin kasar Girka

Shugaban Hukumar bada lamuni ta duniya Christine Lagarde, ta yabawa kasar Girka saboda kokarin da mahukuntan kasar ke yi na shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Shugabar hukumar Bada lamuni ta duniya Christine Lagarde
Shugabar hukumar Bada lamuni ta duniya Christine Lagarde REUTERS/Thomas Peter
Talla

Christine Lagarde na magana ne yau Littini a wani taron Ministocin kudade na kasashen da ke amfani da kudaden Euro game da matakan ceto kasar Girka.

Ta ce yanzu kasar ta Girka ta nuna a shirye ta ke domin a tafi tare da ita kuma za'a tafi da ita.

Ministan Kudin kasar ta Girka Evangelos Venizelos ya nuna fatar cewa kasashen Turai zasu bada kudaden da kasar ta ke bukata, domin ceto ta daga matsalolin da ta ke fuskanta.

Ministocin kudin kasashen na Turai sun duba yuwuwar bada kudaden da suka kai Euro billyon 230, saboda kasar ta Girka ta farfado.

Fira Ministan kasar ta Girka Lucas Papademos ya halarci zaman taron na kasashen Turai domin bada tabbaci kan matakan da kasar ke dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.